Kumbon Juno zai shiga duniyar Jupiter

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar NASA ce dai ta harba kumbon Juno a 2011

Kumbon Juno ya fara sassarfa domin ya samu ya shiga cikin duniyar Jupiter, bayan kwashe shekara biyar da harba shi.

Idan dai har an samu yadda ake so, Juno zai kwashe shekara guda da rabi yana zagaya duniyar ta Jupiter domin sanin hakikanin yadda Jupiter din ta kasance.

Daga nan kuma kumbon zai tarwatse ta hanyar fadawa sararin samaniyya.

A 2011 ne dai hukumar NASA ta Amurka ta harba kumbon na Juno zuwa sama da nufin ya shiga cikin duniyar Jupiter domin gano yadda take.