An yi sallah lafiya a Jamhuriyar Niger

Image caption Shugaban jamhuriyar Niger, Mohamadou Issoufou

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa an yi bikin karamar sallah lami lafiyahar da ma yankin Diffa mai fama da matsalar tsaro.

A ranar Talatar nan ne Musulman kasar suke gudanar da bikin karamar Sallah, bayan ganin jaririn watan Shawwal a ranar Litinin.

Hakan dai ya biyo bayan sanarwar da firai ministan kasar, Briji Rafini, ya bayar, a daren Litinin cewa Talata ce daya ga watan Shawwal.

An dai ce jama'a sun ga jaririn watan ne a sassa da dama a fadin kasar.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da makwabciyar kasar wato Najeriya ta sanar da yin tata sallar, a ranar Laraba.