Dan Afrika Ta Kudu ya lashe gasar Caine

Image caption Lidudumalingani ne ya lashe gasar ta Caine Prize

An bayyana marubuci Lidudumalingani dan kasar Afirka Ta Kudu a matsayin wanda ya lashe gasar rubuta gajerun labarai ta Afirka, wato Caine Prize ta bana.

Gasar dai tana kunshe da tukuicin fam dubu goma na Ingila.

Labarinsa da ya lashe gasar shi ne, 'Memories We Lost', wato 'Abubuwan da Muka Manta Da Su'.

Labarin dai wani mara dadi ne da ya shafi wata al'umma da ta yi kokarin taimakawa wasu iyalai da ke fama da tabin hankali, da ya kunshi camfe-camfe da jahilci.

Labari ne na wata mace da ta shiga tsaka mai wuya saboda 'yan uwanta da suka dade suna fama da tabin hankali.

Jim kadan bayan sanar da lashe kyautar da ya yi, Lidudumalingani ya bayyana matukar jin dadinsa.

A duk shekara ne ake gudanar da gasar rubutun kagaggun gajerun labarai ta Caine Prize, inda ake bayar da lambar yabo ga zaratan marubuta, amma cikin harshen Ingilishi.

A 'yan shekarun nan dai gasar rubutun ta Caine ta zama daya daga cikin hanyoyin zakulo fitattun marubuta a nahiyar Afirka.