An hana shan shisha a Tanzania

Image caption Shan Shisha ya zama ruwan dare a Tanzaniya har mata ma na yi.

An ruwaito firai ministan kasar yana cewa tana lalata rayuwar matasa manyan gobe.

Shisha wacce kuma ake kiranta da hookah ko narghile, hanya ce ta shan sigari da matsa ke yayi a yanzu.

A wani lokacin a kan cakuda ta da kayan marmari da sikari ake kuma shaka ta wani bututu.

Shan shisha dai ya zama tamkar wani ado a shekarun baya-bayan nan a kasar Tanzaniya.

Amma a yanzu an bai wa masu yin wannan sana'a umarnin dakatar da sayar da ita cikin kwana bakwai.

Ana zargin cewa masu shakarta na amfani da kayan maye a maimakon ainihin mahadinta suna zuka.