Me yasa IS ta mayar da Ramadan watan shan jini?

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Kungiyar IS dai tana ikirarin da'awar jihadin Musulunci ne, amma ta kan zafafa kai hari a watan Ramadan

Kungiyar IS ta zafafa kai hare-hare musamman cikin watan azumi, inda ta kashe fiye da mutane 200 a Iraki, yayin da a Bangladesh kuma masu ikirarin cewa su 'yan kungiyar ne suka kashe 'yan kasashen waje 20 a wani gidan cin abinci.

'Yan kungiyar ta IS sun kuma kai hari a filin jirgin sama na Istanbul a Turkiyya inda suka kashe mutane 41. A birnin Riyadh na Saudiyya ma, wasu 'yan biyu masu goyon bayan kungiyar ta IS sun kashe iyayensu saboda sabanin fahimtar addini.

To ko me yasa irin wadannan kungiyoyi ke zafafa kai hare-hare musamman cikin watan azumi.

'Watan tsantseni'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ramadan wata ne na tsantsani da koma ga Allah ba kawai daina ci da sha ba

Watan Ramadan ga al'ummar Musulmi dai wata ne na rahama da jin kai, kuma tsarkakakke.

Musulmai kan shafe kwana 30 ba ci da sha da rana, kuma wata ne da Ubangiji ke yi wa bayinsa rahama da gafara.

Masallatai kan cika taf da masu ibada fiye da watannin da ba Ramadan ba.

Amma ga wasu masu tsattsaurar akidar, suna ganin wata ne na yaki da jihadi.

Sun yi amannar cewa wata dama ce ta ninka ladansu idan suka yi yaki da wayewar da duniya ke ganin ta yi, shi yasa suke kaddamar da hare-hare fiye da yadda suka saba.

A baya-bayan nan ma kungiyar Al-Qaeda da ke Syria ta bayyana watan da, 'watan mamaya.'

A lokacin da watan Ramadan ya gabato kuma, mai magana da yawun kungiyar IS Abu Mohammed al-Adnani, ya shaida wa magoya bayan kungiyar a duniya cewa, ''Ku shirya domin mu mayar da shi watan ganin masifu ga wadanda ba musulmai ba.''

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabannin IS su kan tunzura mabiyansu da cewa Ramadan watan jihadi ne

Ana ganin wannan kira nasa shi ya tunzura magoya bayan kungiyar wajen kai munanan hare-hare a watan azumin.

To amma sai dai ana ganin kungiyar IS na kai wadannan hare-hare wajen ibadar musulmai a lokacin azumin ne saboda ikirarinsu na cewa ba cikakkun musulmai ba ne.

Muhammad Qaddam Sidq Isa, wani mai sharhi ne kan al'amuran gabas ta tsakiya da ke zaune a birnin Dubai, ga kuma sharhin da ya yi kan wadannan hare-hare na IS.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A ranar 28 ga watan Yuni daidai da 23 ga Ramadan IS ta kai hari filin jirgin sama na Istanbul a Turkiyya har mutane 41 suka mutu.

Sai kuma harin da kungiyar ta kai birnin Bagadaza na Iraki ranar Asabar 2 ga watan Yuli, wanda ya yi daidai da 27 ga Ramadan kan wani kantin cin abinci yayin da mutane suka taru don yin sahur, inda aka yi asarar rayuka kusan 200.

Ranar 4 ga watan Yuli daidai da 29 ga Ramadan aka kai wasu hare-hare har uku kasar Saudiyya a rana guda.

Harin farko an kai shi ne kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Jiddah, sai kuma wanda aka kai masallacin mabiya shi'a a Qatif da kuma wanda aka kai kusa da masallacin Manzo SAW a birnin Madina.