Rawar da Birtaniya ta taka a yakin Iraki

Image caption 'Yan Burtaniya da dama sun mutu a Iraqi

A ranar Laraba ne za a kaddamar da wani rahoto kan rawar da Birtaniya ta taka, a kawancen da ta yi da Amurka, a lokacin yakin da Amurkar ta yi yakin Iraki.

A shekarar 2003 ne dai Amurka da Birtaniya da Poland da Australiya suka shiga yaki a Iraki da nufin gano makaman kare dangi da ake zargin Saddam Hussein ya mallaka.

A lokacin ne kuma kawancen sojin ya yi sanadiyyar tumbuke shugaban na Iraki, Saddam Hussain, da kuma zartar masa da hukuncin kisa.

An dai kwashe shekara bakwai ana gudanar da bincike kan rawar da Burtaniyar ta taka kafin shigar Amurka kasar Iraki, da lokacin shigar tata da ma abubuwan da suka faru bayan nan.

Yanzu haka dai an kammala komai kuwa a ranar Laraba 6 ga watan Yuli ne ake sa ran za a wallafa rahoton.

Shugaban kwamitin binciken, John Chilcot, ya yi kashedin cewa ya kamata a rinka yin taka-tsantsan wajen aika sojoji zuwa wata kasa, idan har akwai bukatar yin hakan a nan gaba.

Mista John ya ce "Babban abin da nake fata shi ne yin amfani da sojoji ba abu ne mai yiwuwa ba a nan gaba, musamman ta yadda al'amarin zai tsananta kamar yadda za mu gani a rahoton. Saboda ba a yi lissafi ba wajen yin hakan."

Ana dai ganin rahoton mai kundi 12 zai cancaki wasu mutane da ma ma'aikatun kasar ta Birtaniya.

Sannan kuma rahoton zai ba wa iyalan sojoji fiye da 179 'yan Birtaniyar amsa kan kisan 'yan uwansu, a Iraki.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashin bam a Iraqi

Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda da kai harin da ya fi kowanne muni a Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, bayan wasu hare-haren ta'addanci da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 250.

Birtaniya karkashin jagorancin firai minista, Tony Blaire, ta tura dakaru dubu 28 zuwa Iraki, a inda kuma aka kashe wasunsu da dama.

Hakan ne kuma ya sanya 'yan Birtaniyar suka nemi da a gudanar da bincike kan al'amarin.