Ambaliyar ruwa ta afkawa kudancin China

Ambaliyar ruwa a China Hakkin mallakar hoto China Central Television
Image caption Daruruwan mutane ne suka rasa muhallansu a China.

Kafar yada labaran gwamnatin China ta ce fiye da mutane dari da ashirin ne suka rasa rayukansu sakamakon mako guda da aka shafe ana sheka ruwa kamar da bakin kwarya, lamarin da ya janyo kogin Yangtze da ke tsakiyar kudancin kasar yin ambaliya.

Ambaliyar ruwan ta lalata daruruwan gidaje, da toashe magudanan ruwa da tituna da ta janyo an gagara isa inda mutane suka makale.

An kuma yi kiyasin cewa barnar da ambaliyar ta janyo ta kai dala biliyan sittin. Yawaitar ambaliyar ruwa dai abu ne da aka saba gani a lokaci irin wannan a kasar ta China, sai dai ruwan na bana ya yi barnar da aka dade ba a gani ba.

Masu hasashen yanayi sun ce ta yiwu za a fuskanci ruwa mai karfin gaske a cikin makon nan, kuma gabashin tekun china zai fuskance wata guguwa mai karfin gaske.