Nigeria: Kalubalen da musulmi Igbo ke fuskanta

Image caption An ce musulunci ya je yankin Igbo tun shekaru 200 da suka gabata.

Yankin kudu maso gabashin Najeriya na al'ummar Ibo, wuri ne da addinin Kirista ya kafu, ya yi karfi, kuma mafi rinjayen jama'arsa mabiya addinin na Kirista ne.

To, sai dai duk da haka, akwai 'yan asalin yankin da suka rungumi addinin musulunci, bayan bullarsa yankin tun shekaru kusan dari biyu da suka gabata.

Wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya duba batun shigar addinin musulunci yankin na Ibo da kuma rayuwar Ibo musulmi. Ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti