Messi zai sha daurin wata 21

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Messi zai yi zaman kurkuku na tsawon wata 21

Kafofin yada labaran Spaniya sun ce an yankewa fitaccen dan kwallon nan na kungiyar Barcelona Lionel Messi hukuncin daurin wata 21 a gidan yari.

An kuma yankewa mahaifinsa ma Jorge Messi, hukuncin daurin sakamakon damfarar Spaniya dala miliyan 4.6 tsakanin shekarar 2007 da 2009.

A yayin da ake gabatar da shari'ar, masu shigar da kara sun ce ya yi amfani da kasashen Belize da Uruguay wajen boye kadarorinsa don gudun kada ya biya haraji.

Amma Messi ya ce bai san komai kan wannan lamari.

Kasar Spaniya ce ke tuhumar Messi da kin biyanta haraji na tsawon shekaru.

Messi yana da damar daukaka kara a kotun kolin Spaniya.

Waye Lionel Messi?

  • Shi ne zakaran kwallon kafar duniya sau biyar
  • Shi ne zakaran gasar cin kofin Uefa sau uku
  • Zakaran gasar zakarun Turai a karkashin kulob din Barcelona sau hudu
  • Zakaran La Ligar Spaniya rkashin kungiyar Barcelona sau takwas
  • Ya karbi lambar yabo ta zinare a wasannin Olympics a shekarar 2008 a karkashin kungiyar kwallon kafar kasarsa Argentina
  • Dan wasan da ya fi ci wa Argentina kwallaye inda ya zura kwallo 55 a raga.