Wasu kasashen sun yi sallah cikin matsi

Image caption Jama'a sun yi ta godiya ga Allah duk da cewa an yi sallah cikin halin rashin kudi

A ranar Laraba ne al'ummar musulmi a sassa daban-daban na duniya ke shagulgulan karamar salla watau Eid-el Fitr, bayan kammala azumin watan Ramadan.

To sai dai a wasu kasashen musamman na yammacin Afrika, sallar ta bana na zuwa ne yayin da ake fuskantar matsin tattalin arziki ta fuskar talauci da hauhawar farashin kayaykin masarufi.

Najeriya na daga cikin kasashen da ke fuskantar wannan matsala, kuma lamarin ya fi shafar talakawa, inda wasu ke cewa sun kwashe shekaru da dama ba su fuskanci irin wannan matsi ba.

Hakazalika, wannan matsala ta tabarbarewar tattalin arziki ta sanya jihohin Najeriyar da dama kasa biyan albashin ma'aikatansu a kan kari kuma yanzu haka dumbin ma'aikata a kasar na bikin sallar ne ba tare da sun samu albashi ba.

Wakilinmu Is'haq Khalid ya ziyarci gidan wani karamin ma'aikacin gwamnati a jihar Bauchi domin jin yadda Sallar ta tarar da shi da iyalansa.

Mutumin wanda malamin makaranta ne, ya ce, ''Yadda azumi ya zo mana ba tare da mun yi wani tanadi ba haka sallar ma ta zo mana, komai da ka sani daga kayan abinci zuwa na sawa farashinsu ya hau, ya fi karamin mai karamin karfi irinmu.''

Ya kara da cewa, ''Babban kalubalen shi ne, idan ma na samu albashi a yau to na riga na ci bashi dole biya zan yi ba zan samu damar sayen kayan hidimar sallah ba.''

'Tashin kaya a kasuwanni'

To lamarin dai bai sauya zani a kasuwanni ba, inda a can masu sayar da kaya suke korafin ba sa samun ciniki kamar da a irin wannan lokaci na sallah.

Su ma masu sayen kayan dai duk zancen daya ne, ''Sallar bana ta zo mana a birkice ko yara ma da kyar mu ke hado nan da can don mu ga su dai sun samu kayan sauyawa da sallah.''

Teloli ma bana sun yi ta korafi kan rashin ciniki daga abokan huldarsu kamar yadda suka saba samu a duk shekara.

Sun ce hakan yana da nasaba ne da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriyar.

'Daga Nijar'

A jamhuriyyar Nijar ma wakilinmu Baro Arziki ya duba halin da al'ummar kasar ke ciki musamman masu karamin karfi, kan yadda sallar ta zo musu.

Yawanci wadanda ya zanta da su din dai kan godewa Allah mahallicci ne da ya bar su da rai da lafiya har suka shaidi wannan rana, amma batun tsadar kayayyaki sun ce sai dai a yi kurum

Sai dai duk da haka jama'a da dama ne suka je sayayya kasuwanni a ranar jajibirin sallah don ganin su wadatar da iyalinsu a wannan rana mai girma.

Me ake ciki a Ghana?

A kasar Ghana ma dai al'amarin bai sauya salo ba. Wakilinmu Iddi Ali ya yi hira da wasu mazauna babban birnin kasar Accra, kan halin da Sallar ta riskesu.

Da yawansu kuma sun koka ne kan rashin kudi, balle har a kai ga batun sayen kayan sallah.

Wani mutum cewa yake, ''Ko kudin cefanen sallah bani da shi balle a je ga batun kaya, kaji ma sun yi tsada, lamarin dai sai godiyar Allah kawai.''

Wasu da dama sun ce jallabiya kawai 'yar Saudiyya mai saukin kudi suka sayawa yaransu don su yi kwallaiyar sallah da ita, amma babu batun sabon kaya.

''Amma duk da haka mun gode wa Allah da ya bamu ikon kammala azumi lafiya, har muka ga sallar ma,'' in ji wani da ya zanta da BBC kenan.

Kamaru: Sallah ba naman kaza a tukunya

Jama'a a Yaounde babban birnin Kamaru su ma tasu sallar bata bambanta da ta kasashe makwabtansu irin Najeriya ba, na irin halin rashin kudi da sallar ta zo musu da shi.

A yayin da wasu masu dan abin hannu ke sayen sabon kaya su bai wa teloli dinki, wasu da dama kuwa gwanjo suka yi ta saya don dai kawai a dan sa wani abu da za a kira shi sabo ranar sallah.

Ta bangaren abincin sallah kuwa, a wannan karon jama'a da dama sun sauya naman kaza ne da naman saniya ko kuma kifi don yin abincin sallah.

Wannan sauyin ya biyo bayan takunkumin da yake cigaba da kasancewa a kan naman kaji da hukumomin kasar suka yi, a dalilin bullar cutar murar tsuntsaye wata guda kenan.

Hakan ya shafi hauhawar farashin kaji ga wanda ya dage sai ya yi abincin sallah da su.

Kuma a wannan shekara an samu hauhawar farashin wasu kayayyakin bukata, duk da cewa gwamnati ta yi ta fadakar da 'yan kasuwa da su dinga sassauta wa jama'a.

Sai dai duk da irin wadannan kalubale da ake fuskanta, mutane na cikin walwala da annashuwa na shaida wannan rana mai cike da dumbin albarka ga rayuwar musulmi.