Abubuwan da ake yi kafin sallar Idi

Image caption Musulman duniya na yi sallar Idin bana a ranar Talata da Laraba.

Mutumin da ya yi azumin watan Ramadan, an so ya cika azumin da sallar Idi.

Malamai sun bayyana wasu abubuwa da ake son mai azumi ya yi, a ranar sallar Idi kamar haka.

 • Samun sallar asubar ranar Idi a jam'i
 • Wankan zuwa Idi
 • Bayar da zakkar fidda-kai ga mabukata
 • Cin abinci kafin tafiya masallaci
 • Sanya tufafi masu kyau
 • Tafiya zuwa masallaci
 • Zikiri yayin tafiya
 • Ba a sallar nafila a filin idi
 • Sauraron huduba bayan sallar idi
 • Gaisawa da juna bayan sallah
 • Sauya hanyar tafiya da dawowa
 • Yara da mata da tsaffi duka na zuwa idi
 • Mata masu haila za su iya zuwa salla amma za su tsaya a gefen masallaci