Ban yi laifi ba a yakin Iraqi — Blaire

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Tsohon firaiministan Burtaniya, Tony Blaire da tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton

Tsohon firaiministan Burtaniya, Tony Blair, ya gabatar da wani bayani domin wanke kansa kan al'marin, a inda ya tsaya kai da fata cewa shi fa ba shi ne ya yaudari Burtaniya ta shiga kawancen Amurka na yaki a Iraqi ba.

Amma kuma mista Blaire ya ce har yanzu bai yi da-na-sanin sanya hannu wajen tunbuke gwamnatin tsohon shugaban Iraqin Saddam Hussaini, kuma ko yanzu ne zai sake daukar irin wannan hukunci.

Har wa yau, Mista Alistair Campbell, tsohon shugaban sashen sadarwa ga tsohon firaiministan, ya soki Amurka da cewa babu wani abun azo a gani da Amurkar za ta ce ta cimma bayan mamaye Iraqi.

Shi ma Janar Tim Cross wanda shi ne babban jami'in da ya tsara shigar Burtaniya kawancen Amurka na mamaye Iraqi, ya ce Amurkar ce ta daidaita dakarun kasar ta Iraqi.

Wakilin Burtaniya a majalisar Dinkin Duniya na wannan lokacin, Jeremy Greenstock, ya amince da cewa Amurka ce ta yi wa Burtaniya shigo-shigo ba zurfi wajen yin amfani da karfin soji a Iraqi.

Image caption Tsohon shugaban Iraqi Saddama Hussain

Ya kuma kara da cewa kamata ya yi ace masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun samu isasshen lokaci wajen bincike da gano makamai masu gubar da aka ce Iraqin na da su.

Kawo yanzu dai ma'aikatar cikin gidan Amurka ta mayar da martani kan maganganun.

Mai magana da yawun ma'aikatar, John Kirby ya ce yanzu haka manufar Amurka ita ce samar da zaman lafiya da kuma karya lagon kungiyar masu jihadi ta IS, a Iraqi.

Amurkar ta amince cewa duk da cewa an samu matsaloli sakamakon mamaye Iraqi amma duniyar ta fi dadi da aka kawar da Saddam Hussain.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Janar din sojan Amurka da ya amince yaki a Iraqi kuskure ne.

To amma mai magana da yawun fadar shugaban Amurka mai ci, Barack Obama ya ce su kam dama kowa ya san matsayinsu a kan mamaye Iraqi.

A ranar Laraba ne dai aka gabatar da rahoton binciken da aka yi kan rawar da Burtaniya ta taka a mamaye Iraqi, a inda rahoton ya fito da laifin kowa da kowa fili.

A shekarar 2003 ne Burtaniya ta shiga kawancen Amurka na yaki a Iraqi, a inda ta tura dakaru 28,000.

Wasu kuma daga cikin dakarun ba su samu sun dawo ba sakamakon rasa ransu a filin daga.

Amurka dai ta bayar da dalilan kasancewar makamai masu guba a Iraqi, da makasudin shigarta kasar, al'amarin da ya yi sanadiyyar tumbuke shugaba Saddama Hussain.

Bayannan kuma an zartarwa da Saddama din hukuncin kisa ta hanyar rataya.