Sallah: Mutum tara sun mutu a Ghana

Image caption An bukaci Musulmi su yi hankali kan irin wasannin da za su iya a lokutan Sallah

Mutum tara ne suka mutu lokacin wani turmutsutsi a wajen bikin Sallah a birnin Kumasi na kasar Ghana.

Wakilin BBC ya tabbatar da mutuwar mutanen, kodayake ba a san abin da ya janyo turmututsin ba.

Kazalika rahotanni sun ce mutanen dama suka jikkata na can suka karbar magunguna a asibiti.

Wata jarida da ake wallafawa a shafin a kasar, Pulse, ta ambato babban limanin Ashanti, Shiek Abdul Moman, yana bayyana damuwarsa a kan Musulmin da suka ki yin biyayya ga kiran da aka yi cewa su yi hankali kan irin bukukuwan da za su yi a lokacin Sallah.

Ya kara da cewa bai kamata Musulmi na gari ya rika yin tukun ganganci da shaye-shayen kayan maye da kuma raye-raye ba.