Messi zai daukaka kara kan hukuncin dauri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ya daina buga wa Argentina kwallo saboda ya kasa ci mata kofi

Lauyoyin dan wasan Barcelona Lionel Messi sun ce zai daukaka kara kan hukuncin daurin wata 21 da wata kotu ta yanke masa a kan zargin kin biyan haraji.

Kotun ta Barcelona dai ta kuma ci tarar Messi, mai shekara 29, $2.2m.

Baya ga daurin da zai sha, kotun ta ci mahaifinsa, Jorge, tarar €1.5m a kan cutar da ya yi wa kasar Spain ta €4.1m tsakanin shekarar 2007-2009.

Sai dai ba a sa ran mutanen biyu za su yi zaman gidan-yari.

A karkashin dokar Spain idan aka daure mutum kasa da shekara biyu, to ba zai yi zaman gidan-yari ba

Messi da mahaifinsa za su fuskanci biyan tarar miliyoyin Yuro saboda boye kudadensu a kasashe irin su Belize da Uruguay da ake guje wa biyan haraji.