'Yan sandan Amurka sun kashe wani bakar-fata

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daruruwan mutane ne ke zanga-zanga kan kisan da aka yi wa bakaken-fata

'Yan sandan Amurka sun kashe wani bakar-fata a jihar Minnesota a daidai lokacin da ake yin bore kan kisan da wasu 'yan sandan suka yi wa wani bakar-fata a Louisiana.

An harbe mutumin mai suna Philando Castile a cikin motarsa a lokacin da ya je karbar katin shaidar tuki.

Budurwarsa ce dai ta watsa hoton bidiyo a shafinta na Facebook kai-tsaye a lokacin da 'yan sandan ke harbe shi.

Wannan lamari ya faru ne bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa wani mutum, Alton Sterling ranar Talata.

Daruruwan mutane ne dai suka kwashe dare na biyu suna zanga-zanga a kan kisan da aka yi wa Mr Sterling.

A 'yan shekarun nan 'yan sandan Amurka dai sun yi kaurin-suna wajen kisan bakaken-fata, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan mutanta bakaken-fata da kuma yin amfani da makami ba bisa ka'ida ba.