Baƙaƙen fata sun harbe 'yan sanda a America

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al'amarin ya faru ne bayan kammala zanga-zangar.

Akalla 'yan sanda biyar ne suka mutu sannan shida suka samu munanan raunuka, sakamakon harbinsu da wasu gwanayen harbi suka yi a Amurka.

An dai yi harbin ne yayin wata zanga-zanga da aka gudanar domin nuna kyama kan halayyar kisan bakaken fata da 'yan sandan suka yi a biranen Dallas na jihar Texas da Minnesota.

A karshen zanga-zangar ne kuma hatsaniya ta barke har ta kai ga masu zanga-zangar suka huce takaicinsu a kan 'yan sandan ta hanyar bude musu wuta.

Al'marin ya faru ne da misalin karfe tara na daren Alhamis a kusa da babbar kasuwar birnin na Dallas.

Yanzu haka 'yan sanda sun bazama neman masu hannu a harbi.

'Yan Amurka bakake dai sun sha kokawa kan halayyar 'yan sandan kasar fararen fata wadanda dandanan suke bude wuta a kan bakaken fatar, bisa laifukan da ba su taka kara sun karya ba.