'Yan gudun hijira 6,000 sun fice daga CAR

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana fargabar sake barkewar rikici a kasar

Hukumar kula da 'yan gudun hijira da ke birnin Geneva ta ce sama da 'yan gudun hijira 6000 sun fice daga yammacin Jamhuriyar tsakiyar Afirika zuwa makotan kasashe musamman Kamaru da Chadi.

Hukumar ta ce wannan lamarin ya fara ne tun tsakiyar watan Yuni, lokacin da fada ya barke a tsakanin makiyaya da kuma manoma a garin Ngaoundaye da ke yankin Ouham-Pende.

Lamarin da ya sa aka yi ta kwasar ganima, da kuma kone-konen gidaje.

Hukumar ta kuma bayyana fargabar tayar da sabon tashin hankali a kasar.

Inda ta sake jaddada kira ga kasashen duniya game da tallafin kudaden da take bukata da yawansu ya kai $ 2255 miliyan domin ta samu shawo kan matsalar.