Za a fara taron NATO

Shugabanni a taron NATO Hakkin mallakar hoto
Image caption Za a girke dakaru dubu uku zuwa dubu hudu dan jan kunnen Rasha a kutsen da ta yi Ukraine.

Nan gaba a ranar Juma'a ne shugaba Obama zai gabatar da jawabi a taron kungiyar tsaro NATO a kasar Poland.

Kawancen dai zai kaddamar da girke dakaru dubu uku zuwa dubu hudu a kasashen Estonia, da Lithuania, da Latvia da kuma gabashin Poland.

Wannan shi ne karo na farko da kungiyar kawancen ta NATO za ta girke dakarun ta da nufin jan kunnen Rasha tun bayan hadewar kasar Jamus fiye da shekaru hamsin da suka gabata.

Shi am Firai Ministan Burtaniya David Cameron zai sanar da tallafin fiye da sojoji dari shida da kasar sa za ta bayar domin yin fito-na-fito da Rasha a katsa-landan din da ta yi a Kirimiya da gabashin Ukraine.