'Damunar bana ta yi kyau'

Yayin da musulmi ke kammala shagulgulan sallar Azumi a Nijeriya, yanzu haka hankalin manoma ya karkata zuwa gona inda suke ci gaba da aikace-aikace a lokacin da shuka ta fara tasawa.

Wani manomi da BBC ta tattuna da shi a gonar sa dake ke kauyen Gangarau cikin karamar hukumar Gwiwa a jihar Jigawa, yace damunar bana ta yi kyau, kuma shuka ta fara tasawa, sannan ba su fuskanci wata matsala ba kawo yanzu.

To sai dai manomin ya ce har kawo yanzu ba su samu takin zamani ba da gwamnati ke bayar wa a kan farashi mai sauki, wanda ya ce a yanzu babu abin da suka fi bukata kamar takin dan zubawa shukokin su da suka fara dagowa.

Hukumomin Nigeria dai sun ce suna yunkurin bunkasa aikin noma, dan samar da abinci, da karin samar da kudin shiga, da kuma bunkasa tattalin arzikin manoman.