An sake fasa bututan mai a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsagerun sun ce so suke su durkusar da Najeriya

Masu gwagwarmaya sun sake fasa bututai na kamfanin hakar man fetur na AGIP da ke jihar Bayelsa ta kudancin Najeriya.

Har yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhalkin kai harin.

Sai dai kungiyar tsageru ta Niger Delta Avengers (NDA) ta sha daukar nauyin kai irin wadannan hare-hare, tana mai cewa so take ta durkusar da tattalin arzikin kasar.

A watan jiya ne dai gwamnatin kasar ta ce ta kulla yarjejeniya da kungiyar domin ta dakatar da hare-haren da take kai wa, sai dai kungiyar ta musanta kulla wata yarjejeniya.