Ana cigaba da kashe mutane a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Masu sa-ido a kan al'amuran da ke faruwa a Syria sun ce an kashe kusan mutum 50 a ranar karshe ta yarjejeniyar dakatar da bude-wuta ta kwana uku da Sojojin kasar suka sanar domin bikin Sallar azumi.

Akalla mutum 25 ne suka mutu sakamakon rokokin da 'yan tawaye suka harba kan yankin birnin Aleppo da ke karkashin ikon sojojin gwamnatin Syria, kuma galibin wadanda suka halaka farar hula ne, yayin da sama da mutum 100 suka jikkata.

A bangare guda kuma, an kashe farar-hula 23 a wasu hare-haren da aka kai ta sama kan kauyen of Darkush da ke lardin Idlib, wanda ke karkashin ikon 'yan tawaye, kuma ba a san wanda ya kai hare-haren ba.