Dallas: A na bincike kan mujallar yaki

Image caption 'Yan sada a birnin Dallas na Amurka

'Yan sanda a birnin Dallas na Amurka suna nazarin wata mujalla ta koyan dabarun yaki da aka samu a gidan mutumin da ya kashe 'yan sanda biyar ranar Alhamis.

Masu bincike sun kuma gano wasu abubuwan hada bom, da rigunan silke, da bindigogi da albarusai a gidan Micah Johnson, wanda bakar fata ne da ya taba aikin soja.

Micah Johnson, mai shekara 25, ya bude wuta kan 'yan sandan ne lokacin wata zanga zanga nuna bacin rai kan kisan gilla da 'yan sanda suka yi wa wasu bakaken fata biyu a farkon mako.

Dubban mutane ne suka yi maci a unguwanni a biranen Amurka da dama ranar Juma'a don yin Allah wadai da harbe mutanen biyu.