Niger: Ana zanga-zangar goyon bayan yaki da BH

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin farar-hula sun shirya wata zanga-zangar lumana a Yamai da ma sauran jahohin kasar domin nuna goyon bayansu ga al'umar jahar Difa da sojojin da ke filin daga a fafutukar da suke yi ta yaki da kungiyar boko haram.

A jiya ne dai aka yi zanga-zangar, wadda makasudi shi ne ci gaba da fadakar da duniya game da mawuyacin halin da al'umar yankin ke ciki da kuma muhimmancin da ke akwai na a taimaka musu.

Wasu alkaluma da hukumomin kasar suka bayar dai na cewa sama da mutane dubu 280 ne ke bukatar agaji a jahar ta Difa sakamakon munanan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a yankunansu.

Alhaji Mustapha Kadi na daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar, ya kuma yiwa Baro Arzika karin bayani dangane da makasudun shirya hakan;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti