Sojin Nigeria sun kashe 'yan Boko Haram 16

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kimanin mutum dubu 20 ne suka mutu a shekara bakwai da aka kwashe ana yaki da kungiyar boko haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan Boko Haram 16, a wata arangamar da suka kashe sa'o'i da dama suna yi.

Kakakin sojin Najeriyar ya ce fadan ya barke ne lokacin da wasu 'yan kunar-bakin-wake suka yi yunkurin kutsawa da baburansu wani sansanin sojojin da ke Rann, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

An kashe Sojoji biyu a fadan, ko da yake wasu mazauna yankin sun ce an halaka farar-hula bakwai.

Kimanin mutum 20,000 ne suka mutu a shekara bakwai da aka kwashe ana yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabashin Najeriya, yayin da rikicin ya tilasta wa sama da mutum miliyan biyu barin gidajensu.