An yi jana'izar Shettima Ali Monguno

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Marigayi Shettima Ali Monguno ya taba rike mukamin shugaban kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC

A Najeriya, an yi jana'izar tsohon ministan ma'adinai da man fetur, kuma daya daga cikin magabatan kasar, Alhaji Shettima Ali Mungono, wanda ya rasu ranar Juma'a.

An dai mushi sallah ne a fadar mai martaba Shehun Barno, kuma gwamman mutane ne daga ko ina a fadin kasar suka halarci jana'izar.

Marigayi Shettima Monguno shi ne mutum na farko daya fara rike mukamin ministan mai a Najeriya.

Baya ga kasancewa fitaccen dan siyasa, Dr. Monguno ya kuma yi fice a harkar ilimi.

Marigayin ya taba rike mukamin shugaban kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC a tsakanin shekarar 1972 zuwa shekarar 1973.

Bayan jana'izar marigayin, Dr. Bulama Mali Gubio, tsohon shugaban ma'aikata ne a jihar ta Borno, kuma sakataren yada labarai na dattawan jihar, ya yi wa Haruna Shehu Marabar Jos karin bayani game da wannan rashi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti