'Ban saba wa yan BBOG alkawari ba'

Hakkin mallakar hoto Getty

Fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta mayar da martani dangane da ikirarin da kungiyar da ke fafutukar ceto 'yan matan Chibok, wato Bring Back Our Girls BBOG, ta yi na cewa shugaban kasar ya kasa cika alkawuran da ya yi wa kungiyar shekara guda bayan ganawarsa da mambobinta.

Kungiyar ta BBOG ta ce ta gabatar wa da shugaba Buhari wasu shawarwari yayin ganarwar da ta yi da shi a ranar 8 ga watan Yulin bara, kan batutuwan da suka shafi kubutar da 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.

To sai dai mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labaru, Malam Garba Shehu, ya ce batun ba haka yake ba.

Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa, "Wanda duk ya ce an dau alkawura ba a cika su ba bai yi adalci ga Shugaba Muhammadu Buhari ba."

Ya ce 'yan kungiyar ne ma suka yi wa gwamnati alkawari za su tsara hanyoyin da za a bi wajen tantance mutanen da aka kubutar daga Boko Haram, amma a cewar sa ba su cika alkawarin ba.

Garba Shehu ya ce shugaba Buhari bai san inda yan matan Chibok suke ba, inda ya sani da tuni an kwato su.

" A cikin wannan kungiya akwai wadanda muka san cewa, duk abin da Muhammad Buhari ya yi ba burge su zai yi ba. Shekara guda aka ce sun zauna tare da shi, ai a wannan taron ma shugabannin kungiyar sun gayawa Shugaba Buhari cewa, duk abin da yake ba burge su yake ba," Inji Garba Shehu.

Ita dai kungiyar BBOG ita ce ke fafutukar ganin an kubutar da 'yan matan na Chibok tun lokacin da aka sace su, a watan Afrilun 2014.