An hallaka sojoji da dama a Sudan ta Kudu

Sojan Sudan ta Kudu
Image caption Fada ya barke ne tsakanin sojoji magoya bayan shugaba Salva Kiir da na mataimakinsa Riek Machar

Rahotanni daga Sudan ta Kudu sun ce an hallaka wasu mutane da dama wadanda galibin su sojoji ne a Juba babban birnin kasar a wani artabu tsakanin bangarorin sojojin kasar da basa jituwa.

Wani dan jarida a birnin ya ce an ci gaba da gwabza fada har zuwa sanyin safiyar ranar Asabar kuma yanzu haka ba-shiga-ba fita a Juba.

Wasu rahotanni sun ce dakin da ake ajiye gawarwaki a asibiti ya cika makil da gawarwarkin sojojin da suka mutu.

Fada ya barke ne tsakanin magoya bayan shugaba Salva Kiir da na tsohon abokin adawar sa Riek Machar wanda kuma yanzu shine mataimakin shugaban kasa a jajibirin cikar kasar shekaru biyar da samun 'yancin kai.