Portugal ta ci kofin nahiyar Turai

Image caption Portugal ta cinye kofin kwallon kafa na nahiyar Turai

Portugal ta cinye kofin kwallon kafa na nahiyar Turai, bayan ta doke Faransa da ta karbi bakuncin gasar da ci 1-0, wanda Portugal din ta samu zurawa a ragar Faransa bayan an kara musu lokaci.

Dan wasan Portugal Eder ne ya jefa kwallon a minti na 110, a wasan da aka yi a dandalin kwallon kafa na Stade de France, kuma da wannan ci daya mai ban haushin ya guma wa Faransawa takaici, yayin da magoya bayan Portugal suka yi ta murna da shewa.

Wannan ne dai karon farko da kasar Portugal ta samu nasarar cin wani kofin kwallon kafa mai irin wannan darajar.

'yan wasan Portugal sun yi ba-zata sakamakon rawar-ganin da suka taka, duk kuwa da cewa Zakaransu, wato Christiano Ronaldo bai taka-leda zuwa karshen wasan ba saboda raunin da ya ji a turmin farko ko rabin lokaci.

Tawagar Faransa ce dai ta mamayi wasan, amma ba ta samu sukunin jefa kwallo a ragar Portugal ba.