Japan: Gwamnatin Shinzo Abe ta samu nasara

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Japan, sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi ya nuna cewa gwammatin hadin-gwiwar kasar ta Firayim Ministan Shinzo Abe ta samu rinjaye da kashi biyu bisa ukun kujerun majalisar dattawa.

Da wannan nasarar, Firayim Ministan zai iya yin gyarn-fuska ga kundin tsarin mulkin kasar idan ya ga dama.

Take-takensa dai na nuna cewa yana son Japan ta taka muhiyyar rawa ta fuskar soji yankin, a daidai lokacin da China ke kara karfi, duk kuwa da cewa ya ce ba zai gaggauta yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar ba.

Mr Abe ya ce sakamakon zaben ya nuna cewar al'ummar kasar ta yi amanna da manufofinsa na tattalin arziki.

Ya cigaba da cewa wannan sakamakon zabe zai bamu damar kawo sauye-sauye masu ma'ana wadanda za su ciyar da kasarmu gaba a fannoni daban-daban.