"Rikicin PDP alheri ne"

A Najeriya, har yanzu dai tsuguno bai Ζ™are ba dangane da rikicin da ya yi wa jam'iyyar adawa ta PDP dabaibayi.

Yanzu haka dai jam'iyyar rabe take gida biyu, bangare guda karkashin jagorancin Sanata Ali Modu Shariff, yayin da daya bangaren ke karkashin Sanata Ahmed Makarfi.

Kowanne dai na ikirarin cewa, shi ne halattaccen shugaban jam'iyyar.

Yanzu haka dai kusan za a iya cewa, duk yunkurin sasanta wannan rikici ya faskara.

PDP dai ta soma fadawa cikin rikici ne tun daga lokacin da tasha kaye a zaben shugaban kasa karon farko cikin shekaru 16.

Alhaji Lili Gabari, tsohon dan siyasa ne tun daga jamhuriya ta farko, kuma dan jam'iyyar PDP ne ya yi wa Mukhtar Adamu Bawa karin bayani kan rikicin jam'iyyar ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti