Bangarorin da ke rikici a Sudan ta Kudu ku sasanta- MDD

Hakkin mallakar hoto

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya bukaci shugabannin siyasa a Sudan ta kudu da su tsawatar wa sojojinsu, bayan sabon rikicin da ya barke a Juba, babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Kwamitin sulhin ya nuna damuwa dangane da hare-haren da aka kai kan ofishinsa da kuma sansanonin masu gudun hijira da ke kasar, yana cewa hare-haren ka iya zama laifukan yaki, kasancewarsu barazana ga rayuwar farar-hular da suka fake a ciki.

Fadan dai ya kaure ne tsakanin sojojin da ke goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da masu goyon bayan mataimakinsa, Riek Machar, kuma ana fargabar cewa kasar na iya sake fadawa yakin basasa.

Kwamitin sulhun ya bukaci bangarorin biyu wato sojojin da ke goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da masu goyon bayan mataimakinsa, Riek Machar,da su aiwatar da shirin zaman lafiya.