MDD ta yi tir da rikicin Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakarun wanzar da laman lafiya a Sudan ta Kudu

Kakakin dakarun soji na bangaren mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Riek Machar ya ce dakarun sun ci gaba da gwabza fada da takwarorinsu masu biyayya ga shugaba Salva Kiir.

Kanar William Gatjiath ya shaidawa BBC cewa an kai hari gidan Mista Machar dake Juba, babban birnin kasar, da kuma babban barikinsu.

Ya ce an kashe daruruwan sojoji daga bangarorin biyu tun bayan barkewar rikicin ranar Alhamis.

Kakakin gwamnatin kasar, Michael Makuei ya ce an shawo kan lamarin.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce kura ta lafa a Juba, bayan an shafe sa'o'i da yawa ana musayar wuta.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ta bayyana sake barkewar rikicin a matsayin abin Allah wadai.

Ta ce farafen hula da yawa sun tsere don neman mafaka a harabobin sansaninta.

A cikin watan Afrilu ne Mista Riek Machar ya koma Juba don ci gaba da aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa bayan wata yarjejeniya da aka cimma bara.