Yau ce ranar kula da al'umma ta duniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Yau 11 ga watan Yuli rana ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin duba batutuwan da suka shafi yawan al'ummar duniya.

Bana dai taken wannan rana shi ne 'Inganta rayuwar 'yan mata 'yan shekar 19 zuwa ƙasa.' 'Yan mata dake cikin wadannan shekaru na ƙuruciya dai suna fuskantar ƙalubale iri-iri, da suka haɗa da auren dole, da gaza samun ilimi da za su yi amfani da shi wajen taimakon kansu da kuma al'umma baki ɗaya.

A shekarar 1989 ne majalisar dinkin duniya ta kebe wannan rana domin duba batutuwan da suka shafi yawan al'ummar duniya.