China ta sha kaye a kotun duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata kotun duniya ta yanke hukuncin cewa kasar China ba ta da iko kan tekun Kudancin Sin, inda ta goyi bayan bukatar da kasar Philippines ta gabatar.

Kotun ta ce babu wasu shaidu na tarihi da suka nuna cewa China na da daukacin iko da tekun da kuma sauran amfanin da ke cikinsa.

Kasar Sin ta yi watsi da hukuncin da cewa na "son zuciya ne".

China tana ikirarin iko da dukkan yankin, wanda ke da arziki sosai, ciki kuwa har da wasu tsibirai da wasu kasashen ke ganin cewa mallakarsu ne.

Kotun da ke birnin Hague ta ce China ta keta 'yancin kasar Philippines.

Ta kara da cewa China ta yi "illa ga muhallin yankin" bayan da ta gina wasu tsibirai a yankin.