Theresa May za ta gaji David Cameron

Theresa May
Image caption Theresa May ita ce Sakatariyar Cikin Gida a yanzu

Theresa May za ta gaji David Cameron a matsayin Fira Ministan Birtaniya bayan da ya bayyana cewa zai sauka daga mukamin a ranar Laraba.

Mista Cameron ya bayyana cewa zai halarci muhawarsa ta karshe a matsayin jagoran jam'iyyar Conservative a majalisar dokoki - wacce aka fi sani da Prime Minister's Questions.

Da yake magana a wajen fadarsa da ke Downing Street, Mista Cameron ya ce zai mika takardarsa ta murabus ga sarauniya a ranar Laraba da yamma, a fadar Buckingham Palace.

'Yar takara daya tilo da ke gogayya da Misis May a kokarin maye gurbin Mista Cameron, Andrea Leadsom, ta yanje daga takarar a ranar Litinin da safe.

Mista Cameron, wanda ke kan mukamin tun shekara ta 2010, tun da farko ya ce zai sauka daga mukamin bayan da jama'ar kasar suka kada kuri'ar ficewa daga Tarayyar Turai.

Ya ce zai jagoranci taron majalisar zartarwarsa ta karshe a ranar Talata.