Za a karfafa tsaro a yammacin Afirka

Hakkin mallakar hoto AFP

A Jamhuriyar Nijar, wasu kasashen Afrika ta yamma su biyar da suka hada da Nijar, da Burkina-Faso da Cote d'ivoire da Togo da kuma Benin sun amince su karfafa matakan tsaron da suke dauka domin yaki da ta'addanci a yankin.

Kasashen sun amince su kafa wata runduna ta musamman domin yaki da yan ta'adda a yankin Afrika ta yamma.

Alhaji Ibrahim Yakuba shi ne ministan harkokin wajen Nijar, kuma ya shaida wa BBC cewa tuni shugaban kasar Muhammadou Issofou ya jima da bayar da wannan shawara bisa la'akari da barazanar tsaron da kasashen yankin ke fuskanta.

A cewarsa, barazanar tsaro a yankin na kara yin kamari, don haka akwai bukatar yi wa tufka hanci.