Pelle ya bar Southampton zuwa China

Pelle Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Graziano Pelle shi ne dan wasa na uku da ya bar Southampton a bana

Mai ciwa Southampton kwallaye, Graziano Pelle, ya bar kungiyar, inda ya koma kulob din Shandong Luneng na China da murza-leda a kan kudi fan miliyan 12.

Pelle mai shekara 30, ya koma Southampton daga Feyenoord a shekarar 2014, ya kuma ciwa kungiyar kwallaye 30 a wasanni 81 da ya yi mata.

Dan wasan ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Italiya gasar cin kofin nahiyar Turai da aka kammala a Faransa a ranar Lahadi, ya kuma ci kwallaye biyu a wasannin da ya yi a gasar.

Pelle shi ne dan kwallo na uku da ya bar Southampton a bana, bayan Victor Wanyama wanda ya koma Tottenham da kuma Sadio Mane da ya je Liverpool.

Shi ma kociyan Southampton, Ronald Koeman, ya koma horar da tamaula a Everton a bana.