An bayar da belin Yunusa Yellow

Hakkin mallakar hoto Yunusa Yellow
Image caption Yunusa Yellow ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Wata babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya ta bayar da belin Yunusa Dahiru (Yunusa Yellow) bayan ya shafe wata shida a tsare.

Ana zargin sa ne dai da sace wata yarinya 'yar asalin jihar ta Beyelsa, Ese Oruru, sannan ya aure ta ba tare da amincewarta ba, kodayake ya sha musanta zargin.

Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara.

Kotun dai ta bayar da belin Yunusa ne bayan ya cika sharudan belin da aka gindaya masa.

Sheikh Mujibur Rahman, shugaban kungiyar lauyoyin Musulmi ta Najeriya -- wacce ta shige gaba wajen karbo belinsa --- ya shaida wa wakilinmu Nura Mohammed Ringim cewa wasu 'yan jihar Bayelsa Kiristoci ne suka cika sharuddan belin Yunusa Yellow.

Sharuddan dai sun hada da samun wanda zai tsaya masa mai matakin albashi 16, mai takardar mallakar gida a jihar Bayelsa.