Buhari ya naɗa Hadiza Bala shugabar NPA

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Hadiza Bala jagora ce a kungiyar fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, NPA.

Ma'aikatar sufuri ta kasar ta sanar da cewa an kuma nada wasu daraktoci uku da za su yi aiki tare da Hadiza Bala.

Sanarwar ta kara da cewa nadin na ta zai fara aiki ne tun ranar Litinin 11 ga watan Yuli.

Kafin a ba ta wannan matsayi dai, Hadiza, ta kasance shugabar ma'aikata ta gwamnan jihar Kaduna.

Kuma ita ce wadda ta kirkiro tare da taka rawa a kungiyar nan mai fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok, wato Bring Back Our Girls, tun lokacin Shugaba Goodluck Jonathan.