Hanyoyi biyar da za a iya tunawa da David Cameron

David Cameron Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption David Cameron ya zamo Firai Minista a shekarar 2010

A ranar Laraba ne Firai minista David Cameron zai sauka daga mukaminsa kuma 'yan Birtaniya na shirin yin ban-kwana da shi.

Ra'ayoyin da mutane za su bayyana a kansa za su kasance a kan ficewar Birtaniyar daga Tarayyar Turai, amma kuma ya ya batun irin tasirin da yayi a Afirka?

Ga hanyoyi biyar da za a iya tunawa da shi:

1. Libya - David Cameron tare da takwaransa Nicolas Sarkozy na Faransa a wancan lokaci, na kan gaba a kamfe na kungiyar Nato wanda ya goyi bayan 'yan tawayen Libyan a kan Kanar Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011.

A baya-bayan nan ne dai shugaba Barack Obama ya ce abinda ya faru bayan kamfe din ya daukewa David Cameron hankali wanda kuma hakan ya jefa kasar cikin rudani.

2. Somalia - A shekarar 2013 ne Firai ministan yayi taro a kan Somalia a London, inda ya samu halartar 'yan siyasar Somaliyar da kuma masu fada a ji na kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Theresa May ce ta gaji Mista Cameron

A shekarar 2015 ne ya tura tawagar sojojin Birtaniya zuwa Somaliyar domin su taimakawa dakarun Tarayyar Afirka da ke yaki da kungiyar al-Shabab.

3. Alkawarin tallafi - Mista Cameron ya tabbatar da ganin cewa Birtaniya ta bayar da kaso 0.7 cikin 100 na tattalin arzikinta a matsayin tallafi ga kasashe masu tasowa.

Ya tsaya tsayin daka kan alkawarin duk da matsin lamba da ya fuskanta na a janye tallafin a lokacin da gwamnatin kasar ke fuskantar gibi a tattalin arzikinta.

Ya kuma karfafa wa wasu kasashen gwiwa wajen bayar da irin taimakon da Birtaniyar ta bayar.

4. Cin hanci a Najeriya - Za a iya tunawa da taron da Mista Cameron ya shirya kan cin hanci a shekarar 2016. Kuma gabanin taron ne ya shaida wa Sarauniya Elizabeth cewa Najeriya ce kasar da ta "shahara a cin hanci".

Kasashen Najeriya da Afghanistan sun shahara matuka wurin cin hanci da rashawa.

David Cameron a watan Mayun 2016
Getty

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba ya bukatar Cameron ya ba shi hakuri, sai dai yana so a dawo da kudaden da aka sace daga Najeriya aka kai kasar.

5. Hoton dauki kanka-da-kanka (Selfie) - An yi abubuwa da dama a lokacin da ake taron jana'izar tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela a shekarar 2013.

Amma abu daya da za a iya tunawa da shi, shi ne lokacin da Mista Cameron da Firai ministar Denmark, Helle Thorning-Schmidt da Shugaba Obama suke daukar hoton kansu-da-kansu.

Sai dai mai dakin Obama ba ta ji dadin halin da suka nuna ba.