Fasto zai sha daurin shekara bakwai

Pasto Emmanuel Hakkin mallakar hoto efcc
Image caption Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Mista Emmanuel a gaban kotu

Wata kotu a jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya, ta yanke wa wani Fasto Emmanuel Markus Anga hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari, sakamakon sa munsa da laifin zamba.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta gurfanar da fasto Markus da kuma wani Atin Victor Generous a kotun.

A watan Nuwambar 2013 ne fasto Anga da Mista Generous suka zambaci wani mutum David Madison, inda suka ce su masu hada-hadar musayar kudi ne da zuba jari.

Sun shaida wa Mista Madison cewa idan ya zuba jarin dubu 500, zai samu ribar kashi 10 na kudinsa a watan farko.

Amma daga bisani kudin Mista Madison sun sha ruwa.