Zanga-zanga kan batanci ga mace a Ghana

Image caption Matan sun ce duk namijin kwarai dole ya girmama mace

A ranar Laraba ne wasu daruruwan mata suka yi wata kasaitacciyar zanga-zanga a birnin Accra na kasar Ghana don nuna kara ga shugabar hukumar zabe.

Matan sun fito su nuna rashin jin dadinsu ne kan kalaman batanci da suka ce wani dan majalisar dokoki daga bangaren 'yan adawa ya yi ga shugaban hukumar zaben Misis Charlotte Osei.

Matan sun mika koke ga majalisar dokokin kasar.

Sannan suka kuma bukaci Misis Osei ta dauki matakan ladabtarwa a kan dan majalisar.

A yayin da suke zanga-zangar sun yi ta daga kwalaye masu dauke da kalaman Allah-wadai ga dan majalisar, sun kuma neme shi da ya roki afuwar Misis Osei.

Wata daga cikin matan ta ce, ''Duk wanda bai san girman mace ba, lallai yana bukatar ladabtarwa, ai mace ce ta haife shi, kuma mace yake aure.''

An rawaito cewa dan majalisar ya ce Misis Osei ta sayar da mutuncinta na mace ne don ta samu wannan matsayi na shugabar hukumar zabe.