"FIFA ba ta yi wa Africa adalci ba"

Africa ce ta kadai ta taba kauace wa gsar cin kofin duniya

Shekaru hamsin kenan da aka gudanar da gasar cin kofin duniya na kwallon kafa a Ingila, wanda kuma Ingila ce ta lashe kofin a shekarar 1966. Wani abin da ba a cika batunsa ba shi ne yadda nahiyar Afrika ta kaurace ma gasar, kuma ita ce nahiyar da ta taba daukar wannan mataki.

Ita dai nahiyar Africa ta ki shiga gasar ne sabo da hukuncin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dauka na cewa, daga cikin kasashe 16 da za su kara a gasar, goma za su kasance daga nahiyar turai, biyar daga yankin Amurka da Caribbean, aka kuma barwa kasashen yankunan Africa da Asia da Australia gurbi daya tak, su fafata a tsakanin su, matakin da African ta kalubalan ta.

Bayan wata guda da hukuncin na FIFA, wato a watan Fabrairu 1964, daraktan wasanni na Ghana Ohone Djan ya aika da sakon tangarahu, inda a ciki ya nuna adawa da matakin ya kuma ce ba za ta saɓu ba.

Ya bayyana cewa tsagwaron rashin adalaci ne a warewa nahiyoyi uku gurbi ɗaya, duk kuwa da kudaden da Africa ta kashe wajen wasannin neman cancantar shiga gasar. Dan haka yace ina ma laifin a bawa Africa gurbi daya?

Masana tarihi a harkarar wasanni dai na ganin Africa ta samu ƙarfin gwiwar ɗaukar wannan mtaki ne, sabo da 'yancin da wasu ƙasashen nahiyar suka samu.