'Fasto ya jawo rikici a Zimbabwe'

Image caption Evan Mawarire ya yi ta kiran mutane su fito su yi nuna adawa da yadda ake tafiyar da tattalin arziki

Ana tuhumar wani fasto a Zimbabwe da tunzura mutane su yi rikici, sakamakon kamfe din da yake jagoranta don nuna adawa kan yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin kasar.

Yana amfani da maudu'in #ThisFlag a shafinsa na Twitter, kuma wata jaridar gwamnatin kasar Herald ta sanya a Twitter cewa ana tuhumar Evan Mawarire da neman tayar da zaune tsaye.

A ranar Larabar da ta gabata ne masu fafutuka suka shirya wata zanga-zanga ta zaman-dabado a gida, sun kuma shirya wata makamanciyarta a wannan mako.

Yawanci suna shirya hakan ne a kafofin sada zumunta da kuma Whatsapp, inda suke amfani da maudu'in #ThisFlag.

Tattalin arzikin Zimbabwe ya kara tabarbarewa a baya-bayan nan, inda hakan ya jawo karancin kudi da bata lokaci wajen biyan ma'aikata.