'Yan Boko Haram na 'mutuwa' a gidajen yari

Boko Haram a Kamaru Hakkin mallakar hoto AFP

Mutanen da ake zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne na mutuwa a gidajen kurkuku saboda yunwa da kuma azabtarwa, a cewar kuniyar Amnesty International.

Wani rahoto da kungiyar ta fitar ya ce fiye da mutane 1,000 ne ake tsare da su cikin mummunan yanayi, inda akalla mutane takwas ke mutuwa a kowacce rana.

Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da rahoton, amma kuma ta ce ya kamata a tuna cewar 'yan Boko Haram din sun kashe mutane da dama.

Sai dai kungiyar ta Amnesty ta bayyana cewa Kamaru na kokarin ganin ta rage cunkoso a gidajen yarin da kuma kyautata samar da ruwan sha.

Kungiyar Boko Haram na kai hare-hare da dama a kasar Kamaru, inda take yawan amfani da 'yan kunar bakin wake.

Akalla mutane 500 ne suka mutu a rikicin a bana a Kamaru.

Akasarin 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram na shiga Kamaru ne daga Najeriya mai makwaftaka da ita.