Kotu ta goyi bayan Musulma kan 'dankwali'

Image caption Musulmai a Faransa na yawan kalubalantar gwamnati kan takurawar da take kan sanya tufafin tsarin addini

Wata kotun kare hakkin bil'adama ta Turai ta ce korar da aka yi wa wata Musulma daga aiki a Faransa saboda tana sa dankwali, nuna wariya ce kuma bai dace ba.

Bayan an kori Asma Bougnaoui daga aiki ne sai ta shigar da kara a kotun Faransa, inda daga bisani aka mayar da shari'ar kotun kare hakkin bil'adama ta Turai.

Lauya mai kare ta ya ce, ''hazikar ma'aikaciya ce wadda ta san aikinta a matsayinta ta Injiya, amma aka kore ta a kan wani dalili mara madafa.''

Shari'a sai da ta je har gaban manyan kotunan Faransa, wadanda suka nemi sa bakin kotun kare hakkin bil'adama ta Turai, wadda take yanke hukunci da sa bakin sauran kasashen nahiyar.

Alkalan da ke karbar shawarwari daga masana shari'a ne za su yanke hukuncin a wani lokaci da ba a saka ba.

Musulmai a Faransa na yawan kalubalantar gwamnati da sauran hukumomi a kan takurawar da suke yi wajen sanya tufafin tsarin addini.

A shekarar 2008 ne kamfanin IT Consultancy ya dauki Ms Bougnaoui aiki.