An kashe ministan yaki na kungiyar IS

Image caption Ya taba zama ministan yaki na kungiyar IS

Kungiyar IS ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin manyan kwamandojinta.

Mutumin da kuma ake yi wa lakabi da Omar dan Checheniya, ya yi yaki da dakarun kasar Rasha.

Wata kafar watsa labarai dake da alaka da kungiyar IS mai suna Amaq ta ce an kashe Shishani ne, a gumurzun da aka yi a garin Shirqat, da ke yammacin birnin Mosul a Iraki.

Sunan sa na gaskiya dai shi ne Tarkhan Batirashavili, sai dai an fi sanin sa da Umar Shishani.

Bayanai na cewa babban mai bada shawara ne ga shugaban kungiyar dake da'awar kafa daular musulunci IS Abu Bakar Albagdadi.

A watan Maris ma'aikatar tsaron Amurka dake Pentagon ta ce, ya mutu sakamakon raunin da ya ji lokacin da jiragen yakin Amurka suka yi ruwan wuta a arewa maso gabashin Syria, to sai dai kafar watsa labaran ta Amqa wacce kungiyar IS ke amfani da ita a kai-a- kai ta musanta labarin a lokacin, wacce a yanzu kuma ta tabbatar da mutuwar ta sa.

Kafar ta ce ya mutu ne a kokarin katse hanzarin sojojin da suka kaddamar da hare hare dan kwace iko da birnin Mausul, ko da dai ba ta bayyana cewa yaushe ne ya mutu ba.

A bara Amurka ta yi tayin bayar da dala miliyan biyar ga duk wanda ya kashe shi ko ya bada bayanin inda za a iya samun sa.

Hukumomin na Amurka sun ce ya rike mukaman soja da dama a kungiyar IS, ciki kuwa har da ministan yaki.