Buhari ya kafa rundunar yaki da barayin shanu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura rundunar sojoji ta musamman domin yaki da barayin shanu da 'yan fashi a jihohin Arewa maso Yammacin kasar.

Mayakan wadanda ke boye a dazuka, su kan kai hare-hare kan kauyuka daban-daban.

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali, ya shaida wa BBC cewa a kalla dakarun soji 1,000 ne za a tura nan take, yayin da wasu za su je nan gaba.

Wannan lamari dai ya zamo wani sabon kalubale ga jami'an tsaron kasar, wadanda har yanzu ke cigaba da kokarin murkushe kungiyar Boko Haram.

Akwai tsoron cewa mayakan Boko Haram ka iya shiga cikin wadannan gungun miyagu.

Sharhi, Haruna Shehu Tangaza, BBC Hausa

Image caption Barayin suna boye ne a dazukan Arewa maso Yamma

Barayin shanu da 'yan fashi sun shafe kusan shekaru shida suna addabar yankin Arewa maso Yamma.

Kusan dukkan dazukan da suke yankin babu wanda ya tsira, inda ake sacewa tare da kashe mutane ba dare-ba-rana.

Mutane da dama sun rasa rayukansu, tare da asarar dukiya mai dinbin yawa.

Wannan lamari ya jefa al'ummar yankin cikin mawuyacin hali - ganin yadda maharan ke cin karensu ba babbaka.