Wacece Theresa May

Theresa May Hakkin mallakar hoto
Image caption Theresa May ta shafe shekaru shida a matsayin sakatariyar cikin gida

Theresa May ita ce sabuwar shugabar jam'iyyar Conservative, kuma mace ta biyu da ta kasance Firai ministar Birtaniya.

Za ta karbi ragamar jagoranci a daidai lokacin da kasar ta fada cikin rikita-rikitar siyasa.

An haifi Misis May a ranar daya ga watan Oktobar shekara ta 1956.

Haifaffiyar kauyen Sussex ne da ke Kudu maso Gabashin Ingila, kuma ta girma a Oxfordshire.

Misis May - mai shekara 59, ta yi karatu a makarantun gwamnati, da farko a Wheatley Park Comprehensive School, sannan ta karasa a wata makaranta mai zaman kanta.

Kana ta yi karatu a Jami'ar Oxford.

Majalisar dokoki

Sabuwar Firai Ministar Birtaniya

1956

Ita ce shekarar da aka haifeta

1980

Ta auri Mista Philip May

  • 1997 Ta zama 'yar majalisar dokoki

  • 2010 Sakatariyar cikin gida

  • 2016 Firai Ministar Birtaniya

A shekara ta 1976, lokacin tana shekarar karatunta ta uku a Jami'ar Oxford ne ta hadu da mijinta Philip May, wanda a lokacin shi ne shugaban kungiyar daliban jami'ar ta Oxford.

Sun kuma yi aure a shekara ta 1980.

Ta kuma bayyana maigidanta Philip a matsayin ginshikin rayuwarta.

Bayan da ta kammala karatun digirinta a fannin nazarin labarin kasa, May ta fara aiki a bankin Ingila inda ta samu karin girma a matsayin shugabar sashen lura da harkokin kudi na kasashen, ta kuma shafe shekaru shida.

An zabe ta a matsayin kansila a karamar hukumar Merton da ke kudancin London, kuma ta shafe shekara goma tana shugabancin mazabarta inda ta kara samun mukamin mataimakiyar shugaba.

Misis May ta zama 'yar majalisar dokoki a shekara ta 1997.

Kawo yanzu ita ce sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya tun daga shekara ta 2010.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A lokacin gangamin zaben raba gardama kan ko Burtaniya ta fice daga Tarayyar Turai, ita ta goyi bayan kasar ta ci gaba da zama a Tarayyar Turan ne, sai dai ba ta kasance a gaba-gaba ba.

Masu suka dai, sun ce ba ta da kwarjinin zama firai ministan, amma abokanta sun dage cewa gogewar da take da shi ake bukata.

Irin gogewar da Misis May ke da shi a fannin siyasar Birtaniya ya kara mata tagomashi da samun cancanta, a kuma daidai lokacin da ya dace na zaben raba-gardamar da aka kada kuri'un ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai.

Hakan ya sa ta yi wa sauran abokan karawarta fintinkau.

Theresa May, daya ce daga cikin ministocin da suka fi gogewa da aiki a gwamnatin Birtaniya.

An san ta a matsayin mai aiki tukuru, da za a iya dogaro da ita.

Littattafan girke-girken

Hakkin mallakar hoto Teresa May and PA
Image caption Theresa May a lokuta daban da daban

Ta fada da bakinta cewa, ba ta kashe lokacinta da yawa wajen cin abinci da abokan aiki.

Sai dai Misis May ta samu gagarumin goyon baya a wannan takara.

A 'yan shekarun da suka gabata, ta kasance cikin dambarwa a jam'iyyar Conservative. Daya daga ciki, shi ne shaida wa 'yan jam'iyyar da ta yi, cewa wasu na kallonsu a matsayin marasa kintsi.

A lokacin gangamin zaben raba-gardama kan ko Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai, ita ta goyi bayan kasar ta cigaba da zama a kungiyar, sai dai ba ta kasance gaba-gaba ba.

A lokacin da take matashiya Theresa Brazier, kamar yadda a lokacin ake kiranta, ta fara rayuwarta a karkara, tana kuma shiga irin wasannin raye-rayen gargaijya da mahaifinta ke shiryawa, da kuma aiki a gidan burodi a ranakun Asabar don samun kudin kashewa.

Kamar yadda kawayenta ke mata kirari a lokacin tana matashiya, mace ce mai son ado, musaman na takalma, kuma tun da dadewa tana da burin zama mace ta farko da zata kasance firai minista.

Misis May na sha'war girke-girke, a cewarta ma yanzu haka tana da littattafan girke-girken har guda 100.