Boris Johnson 'makaryaci ne'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mista Johnson ya yi wa 'yan Biritaniya karya a lokacin da ake kamfe din kuri'ar raba gardama na tarayyar Turai

Ministan harkokin wajen Faransa ya bayyana takwaransa sabon ministan harkokin wajen Birtaniya da aka nada, Boris Johnson, da cewa makaryaci ne "kuma yana cikin wani mawuyacin hali."

A wani ra'ayi da ya bayyana a rediyon Europe 1, Jean- Marc Ayrault ya ce Mista Johnson ya yi wa 'yan Birtaniya karya a lokacin da ake kamfe din kuri'ar raba gardama kan matsayin kasar a Tarayyar Turai.

Kuma yanzu yana cikin matsin lamba na ya kare kasarsa.

Ya ce Faransa tana bukatar sahihi da kuma amintaccen abokin yarjejeniya.

Tsohon magajin garin London din ne ya jagoranci kamfe din da ya sa Birtaniyar ta fice daga kungiyar ta Tarayyar Turai.

Nada shi da aka yi a matsayin sabon ministan harkokin waje ya bai wa 'yan siyasa da masu sharhi na duniya da dama mamaki ganin irin kalamansa na nuna wariya da rashin kaunar wasu kasashe.

Har yaznu sabuwar Firai Ministar kasar Theresa May na cigaba da bayyana sunayen ministocinta.